<?xml version="1.0" encoding="UTF-8"?><song><lyrics>[V1]
 1) Ya Allah, kai mai girma ne, kai ne Maɗaukaki,
 Sunanka dai mu girmama saboda jinƙanka.

[V2]
 2) Ya Allah, kai Madauwami, Alƙadiru ne kai.
 Hikimarka da ikonka sun wuce saninmu.

[V3]
 3) Ya Allah, ina tsoronka, tsoro mai ladabi.
 Sujada tawa da bege, tara da kuka ne.

[V4]
 4) Kaunar uwa ko ta uba, dabam da taka ce.
 Ya Ubangiji, ƙaunarka ta fi ta duniya duk.

[V5]
 5) Na gode maka, Allahna, don irin ƙaunarka,
 Tausayinka da hanƙurinka da ni, mai zunubi.

[V6]
 6) Ya Ubangiji, wane mu da za ka so mu fa?
 Mun gode maka, ya Yesu don halin ƙaunarka.

[V7]
 7) Ran da ma duba fuskarka a cikin Sama can,
 Ya Yesu, kai mai ƙaunarmu, sai murna za mu yi.</lyrics>
<title>Ya Allah, Kai Mai Girma Ne LW7</title>
<hymn_number>7</hymn_number>
</song>